Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Na Fushi da Dakarun Saudiya Saboda Kisan Kananan Yara a Yemen


Yarinya karama da ta samu rauni kuma tana fama da cutar kwalara sanadiyar yakin da Saudiya ke jagoranta a Yemen
Yarinya karama da ta samu rauni kuma tana fama da cutar kwalara sanadiyar yakin da Saudiya ke jagoranta a Yemen

Shekaru biyu a jere Majalisar Dinkin Duniya tana zargin kasar Saudiya da kashe yara kanana a yakin da take jagoranta a kasar Yemen

A shekara ta biyu a jere, Majalisar Dinkin Duniya, ta saka dakarun da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen cikin jerin sunayen da take fushi da su, saboda kisan kananan yara da suke yi.

A jiya Alhamis aka gabatarwa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wannan matsaya, a rahoton da ake gabatar mai a duk shekara kan halin da yara ke ciki a wuraren da ake yaki.

Rahoton ya ce dakarun da Saudiyyan ke jagoranta sun kashe ko kuma sun jikkata yara akalla 683 a bara yayin wasu hare-haren sama da aka kai a makarantu da asibitoci, wadanda aka tabbatar da aukuwarsu.

A daya bangaren kuma, a wani jerin sunaye na daban, Majalisar Dinkin duniya ta saka ‘yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran da dakarun Yemen da kuma reshen Al Qaeda da ke yankin kasashen larabawa cikin jerin sunayen da take fushi da su, saboda gazawa da suka yi na kare kananan yaran daga bala’in yaki.

Amma rahoton ya fi dora alhakin kisan yaran akan dakarun da Saudiyyan ke jagoranta, duk da cewa hukumomin Saudiyyan sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin yakin bai shafi yara ba.

A yau Juma’a ake sa ran Jakadan Saudiyya Abdallah-al Mouallim, zai gudanar da wani taron manema labarai.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG