Accessibility links

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Sudan ta janye daga yankin Abyei

  • Ibrahim Garba

Yake-yaken Sudan sun haifar da matsalar cututtuka iri-iri

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci Sudan ta janye dakarunta daga yankin Abyei

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci Sudan ta janye dakarunta daga yankin Abyei da ake takaddama akai, ta kuma cimma yarjajjeniya da Sudan ta Kudu kan makomar yankin na kan iyaka mai arzikin man fetur.

A jiya Alhamis Kwamitin ya kara tsawon zaman dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Abyei zuwa watanni 6. Ya kuma bayyana damuwarsa kan jinkiri wajen kafa hukumar da ‘yan sanda na hadin gwiwa a yankin.

Kwamitin mai mambobi 15 ya yi lale marhaban da janye dakarunta da Sudan ta Kudu ta yi daga Abyei, ta ce yakamata Sudan ta bi sahu ba tare da bata lokaci ko gindaya wasu sharudda ba.

To amman Mataimakin Jakadan Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Idris Ismail Faragalla Hassan, ya ce Sudan ta Kudu ta dau salon da bai dace ba. Y ace yakamata bangarorin biyu su janye a lokaci guda bisa sa idon wata hukuma ta kasa da kasa.

A farkon wannan watan Kwamitin ya yi barazanar kakaba takunkumi ga bangarorin Sudan din biyu, muddun ba su daina fada su ka koma kan teburin shawara ba. Kodayake an takaita tashin hankalin cikin makon da ya gabata, kasashen sun kasa kiyaye wa’adin ranar Laraba, na sake komawa kan teburin shawara.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG