Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Damu Da Hare-haren Nijar


Antonio Guterres, Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.

Akalla fararen hula 290 aka hallaka tun daga watan Janairu, adadin da ya haura yawan mutanen da aka kashe a shekarar 2020 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin da ke gudanar da ayyukan jin-kai, na shirin gudanar da bincike kan irin halin kakanikayi da al’umar yankin Tahoua na Jamhuriyar Nijar suka shiga, sanadiyyar hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin, a cewar mai magana da yawun majalisar Farhan Haq.

Kakakin ya ce sabbin bayanan da suka samu kan harin na ranar Lahadi daga yankin na jihar Tahoua, sun nuna cewa adadin wadanda suka mutu a hare-haren ya kai 137.

Yayin wani taron manema labarai a hedkwatar Majalisar ta Dinkin Duniya a jiya Talata kamar yadda wakiliyar Muryar Amurka Margaret Besheer ta ruwaito, Farhan Haq, ya ce, Majalisar ta lura da yadda hare-haren kungiyoyi masu dauke da makamai suke ci gaba da karuwa a yankunan Tillebery da Tahoua.

Ya kara da cewa, tun daga watan Janairun, an kashe akalla fararen hula 290 a hari daban-daban, adadin da ya ce ya haura yawan mutanen da aka kashe a cikin shekarar 2020 kadai.

Hakan ya sa hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta UNHCR, take shirin kai dauki ga mutanen da hare-haren suka shafa.

Hukumar ta kara da cewa, Nijar, Burkina Faso da Mali da ke yankin Sahel, sun kasance daya daga cikin yankunan da ake ganin saurin karuwar mutanen da aka raba da muhallansu a duniya – inda kididdiga ta nuna cewa, a yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira miliyan uku da suka fice daga gidajensu a cikin kasashensu.

Farhan Haq ya kuma ce, babu shakka batun marawa dakarun kasashen yankin Sahel su biyar baya, na daya daga cikin muhimman batutuwa da ake dubawa.

XS
SM
MD
LG