Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Fara Kaiwa Nepal Dauki


Wasu iyalai da suka rasa matsuguninsu sakamakon girgizar kasa.
Wasu iyalai da suka rasa matsuguninsu sakamakon girgizar kasa.

Biyo bayan bala'in girgizar kasar da ta faru a kasar Nepal da da yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa da kuma jikkata wasu da dama tare da rabasu da muhallansu, Majasisar DInkin Duniya tace ta fara kai gudunmawa a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tace ta fara rabon abinci da magunguna a yau Laraba, a kusa da yankunan da bala’in girgizan kasar Nepal ya auku, inda yanzu haka aka tabbatar da mutuwar mutane sama da dubu biyar.

Wannan tallafi na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Nepal din ke cewa a yau laraba, za su kara kaimi wajen taimakon da ake baiwa wadanda ke bukatar abinci da ruwa da kuma matsuguni.

Yanzu haka, masu ayyukan ceto na ci gaba da kawar da fasassun bangorin da girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta haddasa.

A yammacin jiya Talata, wata tawagar kasar Faransa ta zakulo wani mutum daga burbushin gidansa da ya rushe a Kathmandu, babban birnin kasar, bayan da ya kwashe sama da sa’oi 80 a karkashin buragizan.

Wakilin Muryar Amurka da ke Nepal, Steve Herman yace masu bada agajin gaggawa na kasashen waje sun isa garin Sankhu dake gabashin Kathmandu a yau Laraba, sai dai wani wakilin kasar China yace da wuya a samu wani da rai.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG