Accessibility links

Majalisar Dinkin Duniya Ta Soki Shuwagabannin Sudan Ta Kudu


A man prays at the John Garang Mausoleum before the Independence Day celebrations July 9, 2011 in Juba, South Sudan. (Reuters)

Shugabar hukumar kula da ayyukan kare hakkokin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay, tace ga dukkan alamu dai shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da jagoran ‘yan tawaye Riek Machar, basu damu da matsalolin da yunwa ke janyowa al’ummar yankunan da suke faman rikici a kansu ba.

Navi Pillay ta shaidawa tarobn manema labarai a birnin Juba cewar lallai kam abinda ta gani yana da ban tsoro bayan ta kammala tattaunawar da tayi da shugabannin al’umma, gashi kuma barkewar rikicin da aka faro shi tun watan Disamba ya hana manoma shuka kayan abinci.

Hukumar kula da ‘yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya yanzu haka tana rarraba kayan agaji ga wadaanda suka fi tagaiyyara a dalilin rikicin, sannan hukumar ta bada sanarwar cewa mutanen da yawansu ya kusa kaiwa miliyan biyar ne yanzu haka a Sudan ta kudu ke bukatar agaji matuka gaya.

Rikicin Kabilanci da rigimar da mayakan ‘yan tawaye keyi da sojin Gwamnati a Sudan ta janyo asarar rayukan Bil Adama masu tarin yawa sannan miliyoyin magidanta suna ci gaba da tagaiyyara. Yanzu haka mutane sama da dubu dari hudu ne suka tsere daga gidajensu zuwa kasashen dake Makwabtaka da Sudan.
XS
SM
MD
LG