Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Tantance Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya da Suka Aikata Fyade A Afirka ta Tsakiya


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya yayinda ta ziyarci sojojin kiyaye zaman lafiya a Afirka ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, tace ta tantace sojojin kiyaye sulhu 41 da ake zargi da laifukkan kuntatawa mata a lokacinda suke bakin aiki a Junhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Wani kakakin MDD, Stephane Dujarric, yace 25 daga cikin sojojin ‘yan kasar Burundi ne, 16 kuma daga kasar Gabon suka fito, kuma dukkansu ana zarginsu da aikata laifukkan fyaden da ne a tsakanin shekarar 2014 da shekarar 2015.

Jami’in yace hukuncin da za’a yanke musu zai dogara ne daga kasahen na Gabon da Burundi, wadanda kuma yace ana son a ga sun kaddamarda gagarumin bincike akan wannan lamarin.

MDD dai ta dauki kamar wattani hudu tana gudanarda nata bincike kan wannan lamari, kuma ta maganta da mutane 139 kafin ta bayyana sunayen sojan da abin ya shafa.

XS
SM
MD
LG