Accessibility links

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a kara maida hankali a yaki da zazzabin cizon sauro.


Ana yi ma dan jariri rigakafin zazzabin cizon sauro
Manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun jadada bukatar kara maida hankali a yunkurin kawar da cutar kanjamau, suka kuma ce ana bukatar musamman a fadada ayyukan yaki da cutar da kuma kudaden da ake kashewa a wannan yumurin.

Shugaban babban zauren majalisar Nassir Abdul’aziz Al-Nassir ya bayyana a wani jawabi cewa, tilas ne su dauki kwararan matakai bisa la’akari da matsayin kasashen duniya na kawar da cutar daga doron kasa.

Mr. Al-Nssir ya bayyana cewa, ana samun ci gaba a wannan yunkurin kasancewa an sami raguwar wadanda ke kamuwa da cutar a kasashen da cutar tafi yawa, da kuma tsakanin matasa a duniya baki daya. Yayinda ake kuma samun ci gaba wajen samar da magunguna ga wadanda ke dauke da cutar.

Bisa ga cewarsa, tilas ne a tabbatar da cewa, an cika alkawuran da aka dauka domin a daina yada cutar a kuma magance bukatar kashe kudi domin yaki da cutar nan gaba.
Membobin Majalisar Dinkin Duniya sun yi alkawarin daukar matakan shawo kan yaduwar HIV da nufin kawar da cutar da tayi sanadin mutuwar sama da mutane miliyan dari daga lokacin da cutar ta bulla shekaru 30 da suka shige.
XS
SM
MD
LG