Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Zargi Sudan Ta Kudu Da Keta Haddi


Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon

Ofishin kiyaye hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya yace, gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta aikata abinda ya sabawa siyasar duniya na kashe fararen hula tare da tarwatsa kauyakunsu a yakin basasar kasar.

A sabon rahoton da suka fitar a jiya Juma’a, suka ce dukkan bangarorin mayakan sun aikata tsantsar ta’addanci akan farar hula a cikin dabara, tare da kaucewa daukar laifin da suka aikata.

Musamman a shekarar 2015 lokacin da sojojin ‘yan adawa suka yi rauni. Masu bincike na MDD sun gano cewa sojojin gwamnati da wasu matasa mayakan sa kan bangaren gwamnatin,

sun kai samame zuwa wasu kauyakun da suka yiwa kaca-kaca. Musamman ga wadanda basa goyon bayan gwamanatin kasar.

Babban Kwamishinan Kula da ‘Yancin Bil’adama na MDD Zeid Ra’ad Al’Husain yace, ko yawan rahoton fyade da cin zarafin da aka samu a Sudan din ya isa babban abin misalign da ya fi na ko ina a duniya.

XS
SM
MD
LG