Accessibility links

Majalisar Dinkin Duniya: Yau Ce Ranar Kare Gandun Daji


Wani gandun daji a Jamus.

Tun da dadewa gwamnatin Najeriya da na jihohin su ke tafiyar da wani shiri na kare gandun daji da kuma fadakar da al'ummar kasa kan illar dake tafe da sare bishiyoyi ga muhalli da kuma bil Adama.

Wasu daga cikin shirye-shiryen da ake yi musamman a rana kamar ta yau da majalisar dinkin duniya ta kebe saboda kare gandun daji sun hada da bikin dashen itatuwa a duk shekara.

Gandun dajin Sambisa dake jihar Borno
Gandun dajin Sambisa dake jihar Borno

To amma wasu suna ganin bikin ya gaza wajen kare muhalli bisa ga alakari da tsadar makamashin zamani irin su kananzir da mazauna karkara ke anfani dashi da kuma iskar gas na girki ga mazauna birane.

Tsadar makamashi ne dai ya sanya karuwar masu sayar da itatuwa da gawayi akan manyan hanyoyin Najeriya lamarin dake tabbatar da koma baya na shirin sare bishiyoyi da kuma karuwar kwararowar hamada musamman a arewacin kasar.

To ko menene masana zasu ce akan kwararowar hamada? Menene za'a yi a hana sare bishiyoyi albarkacin wannan ranar da majalisar dinkin duniya ta kebe?

Farfasa Lawal Balarabe na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria masani akan yanayi da harkokin muhalli ya yi fashin baki. Yayi bayani akan illar dake tattare da sare bishiyoyi da kuma abun da yakamata a yi.

Farfasa Balarabe ya ce rashin bin tsari da ka'idoji na gandun daji da kuma na kare muhalli da bin doka su ne matsalolin Najeriya. Yace yanzu fa abu ya zama dole sai 'yan Najeriya sun tashi su fara kare muhalli. Kwararowar hamada gaskiya ce. Tana faruwa ana gani. Itatuwa babu su, kasa kuma tana zaizayewa. Ingancin kasa na taimakawa abincin shuka yana kara raguwa kuma gashi al'umma na kara yawa, ruwa kuma yana kara karanci.Dole a kawo tsarin gyara muhallai.

Akan matakan da yakamata gwamnatoci su dauka wasu suna ganin dole a yi dokoki masu tsanani domin samun mafita. To amma Malam Aminu Maijega kwararre akan raya muhalli yace matsalar bata doka ba ce ta mutane ce. Doka tana nan, mutane ya kamata su kiyayeta. Mutane su mutunta kansu su mutunta doka shi ne mafita.

Ga rahotonBabangida Jibril da karin bayani.

XS
SM
MD
LG