Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Za Ta Yi Taro Kan Hukuncin Amurka a Isra'ila


Babban taron Majalisar Dinkin Duniya
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya

Baban taron Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa na ba sa banba ranar Alhamis domin nazarin shawarar Amurka na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra’ila.

Wakilin Palasdinawa a MDD Riyad Mansour shine ya nemi a gudanar da taron. Wakilan dai zasu sake duba daftarin kudurin nan da Masar ta gabatar da Amurka ta hau kujeran naki akan sa, a ranar Litinin a wani zama da kwamitin sulhu na MDD ya yi.

Jiya Talata ne Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta umarci ofisoshin jakadancin Isra’ila a duk fadin duniya da su shawo kan ma’aikatan jakadanci su hau kujeran naki akan kudurin.

A makon da ya gabata ne shugaban Amurka Donald Trump, ya ce shawarar da ya yanke na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, wadda har za ta kai ga mayar da ofishin jakadancin Amurka can daga Tel Aviv, amincewa ne da abin da ya kamata.

Shi dai wannna kuduri na Masar, bai bayyana sunan Trump ko Amurka ba, amma yace duk wata shawarar ko ‘daukar mataki da zai kawo tashin hankali a birnin Kudus, dole a yi watsi da shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG