Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya zata taimaki Nigeria tinkarar yan gudun hijirar daga Kamaru


FILE - Refugees are seen gathered at Minawao Refugee Camp in northern Cameroon, April 18, 2016. The U.N. refugee agency has called on Cameroon to stop forcibly repatriating Nigerians refugees on its territory.
FILE - Refugees are seen gathered at Minawao Refugee Camp in northern Cameroon, April 18, 2016. The U.N. refugee agency has called on Cameroon to stop forcibly repatriating Nigerians refugees on its territory.

Hukumar lura da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya zata taimakawa Nigeria tinkarar kwararowar yan gudun hijira daga kasar Kamaru

Hukumar lura da yan gundun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace tana yin shirye shiryen yadda Nigeria zata tinkari yiwuwar kwarorowar yan gudun hijira daga kasar Kamaru.

Rikici na kara Kamari a bangarorin kasar ta Kamaru masu magana da turancin ingila, a yayinda ake fama da zaman tankiya tsakanisu da masu magana da harshen Faransanci, wadanda sune suke da rinjaye.

Hukumar lura da yan gungun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kimamin yan gudun hijirar Kamaru dubu biyar ne suka arce zuwa kudu maso yammacin Nigeria bayan da aka murkushe masu zanga zanga a yankunan masu magana da turanci.

Mai magana da yawun hukumar lura da yan gundun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Babar Balcoh ya fadawa Muryar Amurka cewa yana tsoron za’a samu karin yan gudun hijira, a saboda haka ana shirye shiryen taimakon Nigeria tinkarar yawan kwarorowar yan gudun hijiar.

Kusan shekaru guda daya ke nan da mumunar zanga zanga ta barke a Kamaru a lokacinda mazauna yankunan da suke magana da harshen turunci suka fara zanga zangar nuna rashin amincewa akan wariya da daniya da suke zargin hukumomin kasar a bangaren masu magana da harshen Faransanci suke nuna musu

A farkon wannan watan akalla mutane takwas aka bada rahoton sojoji sun harbe su a yankunan guda biyu masu magana da turanci.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG