Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Jihar DamagaranTayi Yarjejeniya da Daliban Jami'a


Daliban Jami'a
Daliban Jami'a

Biyo bayan matsalolin da jami'ar Damagaran ke fuskanta ya sa majalisar dokokin jihar ta kai ziyara jami'ar domin ta shawo kan tabarbarewar ilimi a jihar

Sule Idi mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar ya bayyana cewar sun samu labari da dama bisa tabarbarewar ilimin boko.

Ya cigaba da cewa rahoton baya bayan nan da suka samu na cewa idan ba'a maiada hankali ba tabarbarewar ilimin zai kaiga hana jami'ar cimma muradunta.

Bayan sun tattauna da duka abun ya shafa 'yan majalisar sun yi alkawarin zasu taimaka a yi sulhu tare da kawo daidaito akan alamuran ilimin jami'ar. Sule Idi ya kira mutanen jihar Damagaran da su kawo nasu goyon baya.

Su ma a bangaren jami'an tsaro 'yan majalisar sun zauna da nasu wakilan. Sule Idi yace sun samu wakilansu sun zauna dasu a karkashin gwamnan jihar. Sun bada shawarar kafa wata kungiya ta musamman da zata dinga lura da harkokin ilimi. Duk abun da ya shafi ilimi a shaidawa kungiyar domin ta kawo daidaito. Kungiyar ta tabbatar kowa an bashi hakkinsa gwargwadon yadda doka ta tsayar.

A bangaren daliban jami'ar sun yi bayanin sadawarsu da 'yan majalisar dokokin. Shugaban daliban Adam Ali Ali yace zasu yi yarjejeniya akan biyan daliban idan har za'a iya cigaba ba tare da samun wata matsala ba.

'Yan majalisan sun kira gwamnatin jihar ta daidaita duka matsalolin ilimi a jihar.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

XS
SM
MD
LG