Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Jihar Taraba Zata Binciki Batun Bada Cin Hanci


EFCC
EFCC

Wata sabuwar badakala ta kunno kai a majalisar dokokin jihar Taraba gameda wasu kudade nera miliyan.

Wata sabuwar badakala ta kunno kai a majalisar dokokin jihar Taraba gameda wasu kudade nera miliyan goma da aka ce majalisar ta yi yunkurin baiwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ko EFCC a takaice toshiyar baki domin kada a kame wasu 'yan majalisar.

A yunkurin an ce jami'an EFCC sun yi fatali da tayin. Yanzu su 'yan majalisar sun sha alwashin bincikar kakakin majalisar Josiah Sabo Kente domin ana zargin ta hannunsa ne kudaden suka fita. Mai magana da yawun 'yan majalisar Ishaya Gani yace ba zasu kyale ba

Onarebul Ishaya Gani yace sun san mukaddashin gwamnan ya je taron Transparency International inda ak bashi lambar yabo. Daga baya sun karanta a jaridu cewa kakakin majalisar yayi kokakrin baiwa EFCC toshiyar baki ta nera miliyan goma amma hukumar ta yi watsi da tayin. Sabili da haka yace zasu binciki kakakin nasu ya bayyana masu inda ya samu kudin da kuma su wanene suka sa ya yi tayin toshiyar. Yace suna bincike domin su tabbatar da gaskiyar maganar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG