Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Tayi Yunkurin Dinke Barakar Jam'iyyar a Gombe


APC
APC

A yunkurin kawo daidaituwa tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar Gombe majalisar zartaswar jam'iyyar ta kafa kwamitin sulhu.

Shugabannin APC na kasa sun kafa kwamitin sulhu domin warware takaddamar da ta kunno kai tsakanin 'ya'yan jam'iyyar a jihar Gombe.

Uwar jam'iyyar APC ta shigo domin dinke barakar dake akwai tsakanin jam'iyyun adawa da kuma 'yan jam'iyyar PDP da suka shiga jam'iyyar. Kwamitin sulhun yana karkashin tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Sani Yerima domin ya zauna da su ya kawo sulhu.

Alhaji Tijjani Musa Tumsa sakataren jam'iyyar na kasa ya kara haske kan batun. Yace sun yi muhawara kan al'amarin jihar Gombe. Sun gane cewa lamari ne na siyasar hadaka tunda jam'iyyu dake fafatawa da juna suka hade tare da 'ya'yan sabuwar PDP. Yace yanzu ne za'a zauna a fitar da shugabanni na ainihi da zasu rike harkokin jam'iyyar na shekara hudu.

Da aka tambayeshi ko sun zauna da bangarorin dake korafi, Alhaji Tumsa yace sun zauna dasu sun tattauna da juna. Sun yi muhawara kuma an samu hanyar da za'a cigaba da tafiya tare. Ahmed Mailantarki dan majalisar tarayya kuma jigo a jam'iyyar APC na daga cikin wadanda suka halarci taron.

Mailantarki yace uwar jam'iyyar ta dauki matsayi cewa ba zasu bari abuwa su tabarbare ba a Gombe. Dole a samu masalaha a yi gyaran da yakamata yadda jam'iyya ta tsarasu. Duk ginin da aka yi ba'a kan ka'idar jam'iyya ba za'a rushe a sake lale.

Ga karin bayyani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG