Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Chadi Ta Kada Kuri'ar Karawa Idriss Deby Wa'adin Mulki


Wasu shugabannin kasashen Afrika

Wani bincike da cibiyar nazarin harkokin Afrika -ACSS-ta yi fa arkon wannan shekarar ya gano cewa, kasa da kashi 40 cikin 100 na kasashen Afrika suke aiwatar da wa'adin mulkin da kundin tsarin mulkin kasa ya kayyade.

A cikin wannan makon majalisar dokokin kasar Chadi ta kada kuri'ar gabatar da wani sabon kundin tsarin mulki da zai karawa shugaba Idriss Deby wa'adin mulki na biyu.

Tun a shekarar 1990 Deby yake shugabantar kasar.

Ranar 17 ga watan Mayu al'ummar kasar Burundi za su kada kuri'a kan kwaskwarimar da ka yi wa kundin tsarin mulkin kasar da zai ba shugaba Pierre Nkurunziza da ke shugabancin kasar tun shekara ta 2005 ci gaba da mulki na karin shekaru 16.


A Dimokradiyyar Jamhuriyar Congo kuma, rayuwar al'umma ta kara muni yayin da shugaba Joseph Kabila yaki sauka daga karagar mulki, duk da yake wa'adin mulkinsa ya cika kimanin watanni 18 suka shige.

Duk da hamayya da suke fuskanta daga Amurka da kuma 'yan gwaggwarmaya, batun wa'adin mulki a kasashe 15 shugabannin suka sauka daga karagar mulki bayan cikar wa'adin mulkinsu a cewar sakamakon binciken.

Wanda ya gudanar da wannan binciken ya ce illar wannan za ta iya zama da muni.


Joseph Siegle Darekta a cibiyar ACSS ya shaidawa Muryar Amurka cewa, "rashin wa'adin mulki ya haifar da wani yanayi da sa al'umma ba su iya canza shugabanninsu ta hanyar da kundin tsarin mulki ya tanada.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG