Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Ce Dole Shugaban Kasa Ya Aiwatar Da Wasu Kudurori 12


Dr. Abubakar Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawan Najeriya
Dr. Abubakar Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawan Najeriya

A wani yunkuri na ba saban ba majalisar dokokin Najeriya ta yi ganawar sirri inda ta amince da kudurori 12 da ta ce dole shugaban kasa ya aiwatar dasu cikin kankanin lokaci ko kuma su dauki wani mataki akan shugaban.

A wani yunkuri da ba’a taba yi ba majalisar dokokin Nakeriya, Majalisar ta amince da wasu kudurori 12 da ta ce dole ne shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya aiwatar dasu cikin kankanin lokaci ko kuma su dauki wani mataki a kansa.

Shugaban Majalisar Dattawa Dr Abubakar Bukola Saraki shi ya karanta kudurorin bayan da majalisun biyu sun yi wani zamanba zata cikin sirri na tsawon sa’o’i biyu da rabi.

Kudurorin sun hada da cewa dole ne jami’an tsaro su gaggauta daukan matakin kawo karshen kashe-kashen mutane da ake yi a kasar sannan su kare kaddarorin ‘yan kasa domin hakkin da ya rataya ke nan akan kowace gwamnati.

Majalisun biyu sun kara da cewa suna goyon bayan shugabancin Dr. Bukola Saraki kana sun ce basa goyon bayan shugabancin babban sifeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim K. Idris.

Wasu muhimman batutuwa biyu da suka bude sabon babi a siyasar kasar su ne cewa majalisar zata fara tuntubar Majalisar Dinkin Duniya domin ta gaggauta hanyar ceto dimokradiyar kasar da suke ganin tana tangal-tangal a karkashin mukin Buhari. Daga bisani kuma zasu hada kansu da wasu kungiyoyin duniya masu zaman kansu dake rajin kare Dimokradiya a duk inda ake mulki irnta a duniya.

Dan Majalisa Gudaji Kazaure da aka yi zaman tare dashi y ace babban abun da ya tayar masa da hankali shi ne cewa idan bangaren zartaswa bai yi wani abu ba akan kudurorin ba, zasu yi anfani da duk karfin da majalisa take dashi. Ya ce shi bai yadda da wannan matsayin ba. Yana ganin babu wata hanyar yin maganin bangaren zartaswa sai dai a tsige shugaban kasa, matakin da ba zai yadda dashi ba.

To amma dan Majalisa Abdullahi Balarabe Salami y ace duk abubuwan da suka tattauna sun samo asali daga wasu dalilan ne da bas a jin dadin shugabancin shugaban kasa. A cewarsa mutanen kansu kawai suka sani. Ya ce wata guguwa ce suke gani ta taso inda ayyukan da suka yi can baya zasu rutsa dasu. Saboda haka suna yin anfani da matsayinsu su tara mutane domin a tayasu kuwa.

A saurari rahoton Medina Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG