Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Kara Saba Alkawarin Aiwatar Da Kasafin Kudin Bana


Dambarwar siyasar Majalisar Dokokin tarayyar Najeriya.

Karo na biyu kenan da majalisar Dokokin Najeriya ta gagara cika alkawarin da ta yiwa al’ummar kasa, na cewa zata aiwatar da kasafin kudin da shugaba Buhari ya mika mata tun ranar 22 ga watan Disamba da ta gabata.

Wannan jan ‘kafa da yan majalisar ke yi akan aiwatar da kasafin kudin, yasa akasarin yan Najeriya tunanin ko siyasa ta shiga cikin al’amarin, musammam a wannan lokaci da shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, yake fuskantar tuhuma a kotin kula da da’ar ma’aikata.

Wasu dai na ganin jinkirin ya kara ta’azzara damuwa ta rashin isasshan abinci da tsadar kayan masarufi a kasuwannin kasar.

Sanata Yusuf Abubakar Yusuf ya bayyana hujjar rashin aiwatar da kasafin, inda ya bayyana yadda tsarin da kasafin kudin yakamata ya bi daki daki, kasafin dai zai fara zuwa gurin kwamiti su fara duba shi, sannan a turashi majalisar wakilai bayan nan ya kara dawowa majalisar dokoki, wanda yanzu haka ba a kare aikin sa ba wanda ake sa ran zuwa mako mai zuwa idan Allah ya kaimu za a gabatar da kasafin.

Shi kuma Hon. Garba Garba Chedi, yace akwai wasu yan shirye shirye kalilan wanda ba a karasa ba. ya kuma ce in sha Allahu ranar Talata mai zuwa kasafin kudin zai wuce majalisa.

Kasafin kudin na bana wanda shine kasafin farko na gwamnatin Mohammadu Buhari, wanda ke zaman zakaran gwajin dafi a alamin cika alkawarin da yayi na kawo canji da walwala a kasa.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG