Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Nijar Za Ta Fara Rage Albashin Wasu Mambobinta


Tambarin Jamhuriyar Nijar

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar ladabatar da ‘yan majalisar da ba sa halartar zauran majalisar a-kai-a-kai ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, ta hanyar rage masu albashi, sai dai ‘yan adawa sun ce akwai lauje a cikin wannan nadi.

Sakamakon rashin halartar zaman majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar, shugabannin majalisar sun sha alwashin daukan matakin ladabtar da wakilai da ba sa halartar zamanta.

Matakin da suke shirin dauka shi ne na zaftare kudaden albashi da alawus-alawus da ake bai wa kowane wakili, idan har bai halarci zaman ba.

“Aya ta 10 ta kundin tsarin mulki shi ne yake wannan zance, an ce rana daya idan ba ka zo ba a cire ma wannan hakkin, ita dai majalisar Nijar tun da aka fara ta, ba a taba aiki da wannan kuduri ba.” In ji Kakakin 'yan Majalisa na bangaren PNDS, Sa’adu Dille.

Sai dai ‘yan adawa, wadanda sau tari su kan kaurcewa zaman majalisar na wasu tsawon kwanaki saboda dalilai na banbancin akida, sun ce suna ganin wannan mataki akwai lauje a cikin nadi, Lawwali Ibrahim Mai jirgi, dan majalisa ne na bangaren ‘yan adawa.

“Idan aka sa ka aiki, amana ce ka dauka, ya kamata ka zauna ka yi aiki don ka kula, amma ina amfanin zaman da ba ya iya kare talakansa da cutar da shi da ake yi?” In ji Dille.

Saurari sauran rahoton Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani kan wannan rahoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG