Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai Zata Fara Yunkurin Tsige Shugaban Kasa


Wasu 'yan majalisa suna hawar katangar harabar majalisar domin su shiga zauren taronsu

Sannu a hankali ana kara jan layi tsakanin bangaren shugaban kasa da na 'yan majalisun Najeriya.

Yunkurin da gwamnati tayi ta hanasu shiga zauren majalisar domin su yi taronsu ya sa sun yi anfani da karfin tuwo inda suka balle kofar shiga kafin shugaban majalisar ya samu shiga.

Jajircewar 'yan majalisar, duk da barkonon tsohuwa da 'yansanda suka dinga jefa masu, ya sa sun samu sun yi zaman sa'o'i biyu.

Kafin su watse sun ki su sake duba bukatar shugaban kasa akan sake sabunta dokar ta baci a jihohn Borno, Yobe da Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya. Maimakon haka ma sun fara shirin tsige shugaban ne.

Oanarebul Sha'aibu Gwanda Gobir yace sun fara sa takardar tsigewa ko korar shugaban kasa domin ya kasa tsare tsarin mulkin kasar. Shugaban ya kasa kare 'yan Najeriya daga hare-haren Boko Haram. Shugaban ya rage darajar kasar a idon duniya. Bai cancanta ya shugabanci jama'a ba. Idan yana son ya zama shugaban Ijaw sai ya je ya zama shugaban Ijaw din.

Yadda jami'an tsaro suka kutsa harabar majalisar ya kasance abun damuwa ga 'yan majalisar da dama. Yin hakan katsa landan ne ake yiwa dimokradiya.

Yanzu dai dokar ta baci ta sha ruwa domin ta kare yau saidai shugaban ya sake tuntubar majalisar da wata wasika.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG