Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Ta Amince da Kudurin La'antar MDD Kan Israila


Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Paul Ryan

Majalisar Wakilai ta Amurka ta amince da wani kuduri na la’antar M-D-D kan kuri’ar da ta zartas kwanan baya, tana caccacakar Isra’ila kan gidajen da take ci gaba da ginawa Yahudawa a cikin yankunan Palesdinawa.

Wakilai 341 suka amince, wasu 80 suka ki amincewa da kudurin (da ba dole ayi aiki da shi ba) wanda majalisar wakilan Amurka din ta zartas jiya Alhamis, inda take jadadda goyon bayanta ga Isra’ila da kuma kin goyon bayan duk wani matakin da MDD zata dauka dake nuna kyama ga kasar ta Bani Yahudu.

A cikin watan jiya ne dai Amurka tayi abinda ba ta saba ba, ta kebance kanta daga jefa kuri’a lokacinda aka zo neman kuri’un kasashe gameda sukar lamirin Isra’ila kan wadanan gidajen da take ginawa wa ‘yan kasarta a yankunan na Palesdinu.

A duk inda aka fiton nan, galibi Amurka ta kan yi anfani da karfin kujerar nakin-ta ne wajen toshe duk wani yunkuri na sukar lamiri ko la’antar isra’ila.

Wasu na ganin matakin janye jikinta daga jefa kuri’a din kamar wata alama ce dake nuna niyyar Amurka, a karkashin gwamantin Barack Obama mai shirin sauka daga mulki, na nuna matsayarta kan wainar da ake toyawa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG