Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Na Gudanar Da Bincike Kan Batar Bindigogi Dubu 178,459


Majalisar wakilan Najeriya (Facebook/ Majalisar wakilai)

Majalisar Wakilan Najeriya ta kwaranye raderadin da aka yi cewa batun batar bindigogi dubu 178,459 a rundunar 'yan sanda zai wuce salun-alun.

Majalisar wacce dama ta kafa kwamiti na musamman bayan samun rahoton batar makaman daga mai binciken kudi na kasa Adolphus Aghughu, ta ce sam batun ba zai bi ruwa ba.

A zantawar sa ta musamman da Muryar Amurka, shugaban kwamitin 'yan sanda na majalisar wakilai Usman Bello Kumo ya ce majalisa ba za ta yi sake da irin wannan batun da ya shafi lamuran tsaro ba a daidai lokacin da Najeriya ke kakkabe 'yan ta'adda daga Arewa da Kudu maso Gabashin kasar.

Usman ya bukaci jama'a da su kwantar da hankalin su don ba za a bar akasin ya kawo koma baya ga kare rayuka da dukiyoyin al'umma ba.

Shi kuwa, kwararre a lamuran tsaro Dokta Kabiru Adamu ya ce bincike na da muhimmanci don zai gano gaskiyar halin da rundunar 'yan santa ta ke ciki don kaucewa fadawar makamai hannun miyagun iri.

Amma ra'ayin mukadashin kwamishinan ‘yan sanda Ali Alhassan Fagge mai ritaya ya sha banban, don yana ganin makaman ka iya bata ta hanyar hatsarin da 'yan sanda ke fuskanta ne a fagen aiki.

Ba wani sabon labari ba ne cafke jami’ín tsaro a Najeriya da hannu a aikata miyagun laifuka ko hada kai da miyagun iri wajen kisan gilla da neman kudi ko ta halin kaka.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Ce Ba Za Su Daina Batun Batar Bindigogi Dubu 178,459 Ba
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00


Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG