Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majami’ar Katolika A Jihar Adamawa Ta Tallafawa Mata ‘Yan Gudun Hijira


Bishop Mamza Na Dakon Hatsi Don Rabawa Ga 'Yan Gudun Hijira

Mata masu juna biyu da wadanda ke shayarwa masu zaman gudun hijra dubu uku da dari biyar suka ci anfana daga tallafin hatsi da kayan masarufi da majami’ar Katolica dake Yola jihar Adamawa tare da hadin gwiwar kungiyar MUSIYO ta kasar Jamus domin tunawa da ranar jinjinawa kungiyoyin agaji dake bada kula ga wadanda tashe-tashen hankula da yaki ya shafa.

Bishop Stephen Dami Mamza na darikar Katolika ya shaidawa muryar Amurka ya ce, suna kwaikwayon ayyukan agaji da Mama Teresa ta kasar Indiya da Paparoma ya aiyana waliyiya makon jiya saboda ayyukan agaji da ta aiwatar kafin rasuwarta a shekara ta 1997.

Ya ce rabon tallafin gida-gida ya biyo bayan la’akari da majami’ar ta yi na mafi yawan lokuta tallafin da kungiyoyi ke bayarwa baya isa ga rukunin ‘yan gudun hijira da suka sami mafaka a gidajen ‘yan uwa da dangi.

Wasu daga cikin matan da suka anfana daga tallafin sun fada cikin hirar su da wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu, sun nuna farin cikinsu da kungiyar ta bi su da tallafin har gida kamar yadda zaku ji malama Hauwa Isa da Tani John ke fadi cikin wannan rahoton cewa shine karon farko da irin wannan tallafi ya shiga hanunsu.

Saurari rahotan Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG