Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majilisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Abar 'yan Jarida Suyi Aikin Su

Georgia -- Georgian journalists protests against the detention of their Azerbaijani colleague in Parliament. Tbilisi, 06Jun2017
Georgia -- Georgian journalists protests against the detention of their Azerbaijani colleague in Parliament. Tbilisi, 06Jun2017

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci aba yan jarida daman shiga Yemen biyo bayan hanawa manema labaran BBC guda uku shiga kasar da dakarun hadin guiwa karkashin jagorancin Saudia masu yaki da yan tawayen Houti.

Yan jaridar suna cikin jirgin ma’aikatar kai agaji na Majalisar Dinkin Duniya dake kan hanyarsa zuwa babban birnin kasar Sana’a a shekaranjiya Talata, amma sai aka hana jirgin tashi a Djibouti saboda yan jaridan dake ciki.

Mataki irin wannan bashi da amfani. Wannan shine babban tsaiko da aikin kai kayan taimako ke huskanta daga mutane. Duniya na bukatar su san abin dake faruwa kuma yakamata yan jarida su samu daman shiga, a cewar kakakin Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq a jiya Laraba.

Haq yace jirgin kai kayan taimakon da aka hanashi tashi a ranar Talata, an riga an bashi izinin sauka Yemen a jiya Laraba, amma bada manema labaran na BBC ba.

Rahotanni sun ce yan Saudia sun ce basu da tabbacin kare lafiyar ma’aikatan na BCC.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG