Accessibility links

Majo Hamza Al-Mustapha Ya Koma Gidanshi A Kano

  • Grace Alheri Abdu

Wani dangin Maj. Hamza Al-Mustapha yana kuka bayan hukumcin da aka yanke a Lagos bara

Dubban magoya baya, da 'yan'uwa da abokan arzikin Majo Al-Mustapha sun yi mashi gagarumar tarba a birnin Kano

Dubban masoya, ‘yan’uwa da abokan arziki sun yi dafifi a tashar jirgin saman kasa da kasa na Aminu Kano dake birnin Kano jiya domin tarbar Majo Hamza Al-Mustapha wanda kotun daukaka kara ta wanke bayan ya shafe shekaru goma sha hudu a gidan yari bisa zargin kashe Kudirat Abiola matar tsohon hamshakin dan kasuwan da aka kyautata zaton shine ya lashe zaben shekara ta dubu da dari tara da casa’in da uku.

Bayan saukarsa daga jirgi kafin isarsa zuwa gida, Majo Hamza Al-Mustapha ya fara yada zango a gidan gwamnatin jihar Kano da fadar Sarkin Kano da kuma gidan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Sani Abacha inda ya kai gaisuwar bangirma, daga nan ya wuce makabartar kofar Mazugal inda aka yi addu’a ta musamman ga mahaifansa da aka binne a can.

Daga bisani Majo Hamza Al-Mustapha ya yi jawabi ga dumbim wadanda suka fito tarbarshi a kofar gidanshi dake Lamido Rod a birnin Kano.

XS
SM
MD
LG