Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makamai Sun Fada Gidajen Jama'a Sakamakon Fafatawa Da Boko Haram A Maiduguri


Makamai Masu Linzami Sun Fada Cikin Gidaje Sakamakon Fafatawa da Boko Haram
Makamai Masu Linzami Sun Fada Cikin Gidaje Sakamakon Fafatawa da Boko Haram

Sakamakon wata arangama tsakanin jami'an sojin Najeriya da wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne, wasu makamai sun fada kan wasu gidaje biyu a anguwar Bintu Suga dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Jami’an sojin Najeriya sun ce sun samu nasarar kashe wasu 'yan Boko Haram su 9, tare da kwace makamai 2.

Makami Mai Linzami ya Fada Cikin Gidaje
Makami Mai Linzami ya Fada Cikin Gidaje

Wani mazunin unguwar Binta Suga Muhammad Musa wanda lamarin ya shafa, ya shaidawa wakilin muryar Amurka cewa yana zaune a kofar gidansa da misalin karfe shida da kusan minti talatin, yaga wata wuta daga sama ta taso ta fada cikin gidan sa, amma babu wanda ya mutu ko ya sami wani rauni. Sannan ya ce jami’an ‘yan Sanda da Soji duka sun zo sun duba yanayin.

Makami Mai Linzami ya Fada Cikin Gidaje
Makami Mai Linzami ya Fada Cikin Gidaje

Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya Kanal Sagir Musa ya tabbatar wa da wakilin muryar Amurka faruwar al’amarin ta wayar Tarho. Ya ce, a lokacin da rundunar sojin Najeriya ke musayar wuta da ‘yayan kungiyar Boko Haram ne lamarin ya faru. Kuma bututun harba Bom ne ya fada a gidajen, ba ainihin Bom din ne ya fada ba.

Ya kara da cewar, rundunar sojin Najeriya ta je ta ganewa idon ta irin asarar da akayi, kuma za su yi kokarin ganin an taimakawa wadanda ibtila’in ya shafa.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG