Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makarfi Ya Mika Shugabancin PDP Ga Secondus


A lokacin taron PDP na bangaren Sanata Ahmed Makarfi
A lokacin taron PDP na bangaren Sanata Ahmed Makarfi

An mika dawainiyar gudanar da hidindumun babbar jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya ga sabbin shugabannin da aka zaba.

Rahotanni daga Najeriya na cewa shugaban kwamitin gudanarwar jam’iyar PDP na rikon kwarya ya mika ragamar tafiyar da jam’iyar ga zababbun shugabannin jam'iyar.

Sanata Ahmed Makarfi da sauran masu rike da mukamai a kwamitinsa, sun mika ragamar ne a yau Litinin kamar yadda shafin sada zumuntar jam'iyar ta PDP na Twitter ya nuna.

A ranar Asabar din da ta gabata, PDP ta gudanar da babban taronta a Abuja, babban Birnin Najeriya.

An kuma zabi Prince Uche Secondus a matsayin shugaban jam’iyar bayan da ya doke abokanan hamayyarsa.

Raymond Dokpesi da Farfesa Adeniran ne suka fafata da Secondus, inda suka soki sakamakon zabin.

Secondus ya samu kuri’a 2,000 yayin da Adeniran ya samu kuri'u 230 shi kuma Dokpesi ya samu 66.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG