Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mako Guda Da Rufe Filin Jiragen Sama Na Abuja


Aikin gyaran filin saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke Abuja ya kankama, yayin da aka karkatar da saukar jiragen zuwa jihar Kaduna.

Yau dai mako guda kenan da rufe filin jiragen na babban birnin tarayya domin yi masa gyara. A cewar Injiniya Saleh Dinoma, shugaban hukumar filayen saman Najeriya, yanzu haka ana nan ana gudanar da aiki a tashar jiragen.

Wakilin Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, ya ziyarci filin saukar jiragen na Abuja domin ganin yadda aiki yake wakana, inda yace yaga manyan motocin da ke gudanar da aikin wasu na banbare hanyar da jirgi yake sauka domin maye gurbinta da sabuwa.

To sai dai masu hada-hadar kasuwanci a filin jiragen saman na Abuja, na kokawa game da wani hali da suka shiga na rashin ciniki, wadanda yanzu haka ke fatan za a kammala wannan aiki cikin wa’adin da aka shata.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG