Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makon Karshe Na Yakin Neman Zabe A Amukar Ya Zafafa


Yakin neman zabe na kara zafafa, a daidai lokacin da ake makon karshe kamun babban zaben.

Yayin da ya rage 'yan kwanaki kafin a kada kuri’ar karshe a zaben shugaban kasa na Amurka, manyan 'yan takarar kasar biyu sun maida hankali kan yakin neman zabe a jiya Alhamis a jihar Florida da ke kudu maso gabashin kasar.

Biden ya soki shugaba Donald Trump, akan yin tarukan yakin neman zabe na mutane da yawa a daidai lokacin da ake fama da annobar Korona inda galibin wadanda suke zuwa taron, ba sa sanya takunkumin rufe hanci da baki, ya na mai kiran tarukan “wuraren yada cutar sosai”

Trump, a lokacin da ya ke magana a wajen wani taron jama’a, a wani filin wasanni a birnin Tampa, ya kara yin hasashen cewa 'yan Republican masu kada kuri’a da yawa za su fita yin zabe ranar 3 ga watan Nuwamba.

"Mu za mu lashe wannan zabe da gagarumar nasara, ku tsaya kuma ku gani." Shugaba Trump ya yi hasashe.

Yayin jawabin da ya yi a Tampa, Trump ya kuma ce nan da ‘yan makonnin za a samu rigakafin COVID-19 a Amurka, ya kuma yi alkawarin cewa masu manyan shekaru za a fara ba riga-kafin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG