Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malala Ta Bukaci A Kaddamar Da Dokar Ta Baci Domin Bunkasa Ilimi A Najeriya


A ziyarar ta Najeriya, Matashiyar nan mai kamfe kan raya ilimi a duniya Malala Yousafzai, ta yi kira ga hukumomin Najeriya, su kaddamar da dokar ta baci domin dagewa wajan bunkasa harkokin ilimin yara maza da mata, kuma duk kudin da za’a kashe akan lamarin a bayyanasu a fili.

Da take jawabi jim kadan bayan ganawa da mukaddashin shugaban Najeriya, farfesa Yemi Osinbajo, a fadar Aso Rock, Malala Yousafzi, ‘yar kasar Pakistan, data yi suna a duniya bayan ‘yan kungiyar Taliban sun yi yunkurin hallakata ta wajan harbinta da bindiga, ta cigaba da kamfe dinta na neman bunkasa ilimi a duniya.

Kamfe din Malala, na nuni da mayar da hankali akan muhimmanci da fahimtar yadda malami daya da alkalami daya ka iya canza duniya ta aminta daga jahilci.

Wannan shine karo na biyu da matashiyar ta ziyarci Najeriya, kuma ziyarar ta ta farko shekarar 2014, ta gana da masu fafutukar sakin daliban ‘yan matan Chibok, da kungiyar boko haram ta yi garkuwa da su, ta bada gudummuwa daga asusun ta na ilimi inda ta sami ganawa da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.

Malala ta bayyana farin cikin ta akan yadda hukumomi da mukaddashin shugaban kasa suka aminta da wannan kira nata.

Daga Abuja, Nasiru Adamu El-hikaya nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG