Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Tunawa Da Tsohon Shugaban Afirka Ta Kudu Nelson Mandela


Ranar 18 ga watan yuli rana ce da majalsar dinkin duniya ta ware domin tunawa da dr Nelson mandela, tsohon shugaban Afrika ta kudu kuma jagoran kwatowa bakaken fata ‘yanci daga turawan wariyar mulkin mallaka a Afirka ta kudu.

Nelson Mandela, ya kwashe shekara da shekaru yana gwagwarmaya domin kawo samun ‘yancin kasar daga turawan mulkin mallaka da kuma kawo karshen nuna banbanci da wariyar launin fata, ko yaya wasu ‘yan Najeriya ke ganin wannan jan gwarzo?

Jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyin su musamman ganin yadda wannan shugaba ya sha gwagwarmaya domin kwatarwa kasar sa ‘yanci daga turawan mulkin mallaka.

Idan aka kwatanta tarihinsa da ci gaban da kasar ta Afirka ta kudu ta samu, akwai darussa da dama da suka kamata shugabannin kasashen Afirka, su yi koyi da su, ganin yadda har kasa ta nade baza a taba mantawa da shi ba.

Taken bukin na wannan shekarar shine tashi tsaye domin yaki da talauci da kuma tabbatar da dai-daito ko adalci a tsakanin al’ummar duniya baki daya.

Daga Legas wakilinmu Babangida jibrin da da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG