Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man fetur din da Najeriya ke samarwa ya yi kasa da kusan kaso 40, sakamakon tada kayar bayan 'yan Neja-Delta da kai hare-hare, kamar yadda karamin ministan mai Emmanuel Kachikwu ya bayyana. Kamar yadda ya sanar da manema labarai a zauren ‘yan majalisar wakilai a yau Litinin.

Inda yace yanzu samar da gangar man da aka saba na yawan da ya kai Miliyan 2 da digo 2 ne kawa a rana. Yanzu an koma ana samar da ganga Miliyan 1 da Dubu Dari Hudu ne kawai a rana, sannan kuma akan Dalar Amurka 38 bisa farashin kowace gangar mai.

Ana asarar ganga kimanin Dubu Dari Takwas kenan a kullum. Najeriya dai ta ta’allaka ne ga yawan gangar man da take samarwa a kullum, wanda ko kasafin kudin bana na shekarar 2016 yayi hasashe ne bisa samuwar gangar mai Miliyan Biyu da Dubu Dari Biyun da ake samu a da.

‘Yan tsageran sun shafe shekaru fiye da 10 suna fasa butun da satar gangunan man kasar ko kuma bata wuraren da na’urorin hakar mai suke a yankin.

Karshe ministan yace gwamnati zata dubi lamarin afuwar da aka yi musu a baya. Tare da nuna Najeriya zata kashe kudi akan bangaren man kasar.

XS
SM
MD
LG