Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester City Ba Ta Da Bukata Da Messi


Lionel Messi

Kungiyar kwallon kafar Manchester City ta Ingila ta nisanta kan ta da rahotannin da ake bazawa, da ke ta’allaka ta da zawarcin shahararren dan wasan Barcelona ta kasar Spain, Lionel Messi.

Messi dan kasar Argentina, zai karkare kwantaraginsa a Barcelona a bazara mai zuwa, inda kuma alamun ficewar kungiyar daga gasar Zakarun Turai da wuri, ya kara uzzura rade-radin cewa zai bar kungiyar.

To sai dai akwai rashin tabbas sakamakon zaben da ake gudanarwa na shugabancin kungiyar ta Barcelona, a yayin da dukkan ‘yan takara 3 na mukamin suka bayyana kudurinsu na ci gaba da rike dan wasan.

Messi mai shekaru 33 da haihuwa, ya lashe lambar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon D'Or har sau 6.

Lionel Messiya lashe Ballon d'Or sau 6
Lionel Messiya lashe Ballon d'Or sau 6

An dade ana rade-radin yiwuwar komawar sa a kungiyar City musamman saboda dangantakar sa da tsohon kocinsa Pep Guardiola, duk da yake kuma wasu rahotannin na cewa kungiyar Paris St-Germain ta kasar Faransa ma tana sha’awarsa.

An ba da rahoton cewa City ta yi tayin dan wasan da ihsani mai tsoka, to amma kuma kungiyar ta ce ba gaskiya ba ne, ba wani tayi da ta yi wa Messi a yanzu da ma can baya.

'Yan Wasan Manchester City
'Yan Wasan Manchester City

Messi ya bukaci barin Barcelona a watan Agustan shekarar da ta gabata, to amma kuma shugaban kungiyar na wannan lokacin Josep Maria Bartomeu ya toshe kafar tafiya ga dan wasan.

Abubuwan Bajinta Biyar Da Har Yanzu Lionel Messi Ke Zarra Kai
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:40 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG