Accessibility links

Manchester United Ce Ta Daya A Duniya


Wayne Rooney (dama) da Michael Carrick na kungiyar Manchester United

Duk da cewa bana ba ta lashe kofin Premier League ba, Manchester United ta samu kambun Kungiyar Wasa Mafi Daraja A Duniya

Kamar yadda duk mai karanta wannan zai iya sani, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi hasarar kambun Premier League na wannan shekara a ranar karshe ta wasannin lig-lig na Ingila, a lokacin da abokiyar hamayyarta Manchester City ta tsamo kitse a wuta a kan ‘yan wasan Queens Park Rangers a watan Mayu.

Amma har yanzu, kungiyar Manchester United ce take rike da wani da wani kambun: na Kungiyar Wasa Da Ta Fi daraja A Duniya Baki daya!. Kamfanin Forbes yayi kiyasin cewa a yanzu, darajar kungiyar Manchester United ta kai ta Dala Miliyan dubu biyu har ma da karin miliyan 230.

Kungiyar Wasa da ta zo ta biyu a duk duniya, ita ce Real Madrid ta kasar Spain, wadda aka kiyasta darajarta a kan Dala Miliyan dubu 1 da miliyan 880.

Da ma dai kungiyar Manchesater United ba bakuwa ba ce wajen rike wannan kambu na wadda ta fi daraja a duk duniya.

A bayan kudaden shiga da take samu na ‘yan kallo da telebijin da wasunsu, Manchester United tana samun wasu kudaden shiga kamar haka:

1. Kamfanin Inshora na Aon yana biyanta Dala miliyan 31 a shekara domin a sa sunansa a jikin rigar ‘yan kwallon Man U.

2. A bara kamfanin DHL Express ya kulla yarjejeniyar sanya sunansa a jikin rigar furatis na Man U a kan dala miliyan 62 kowace shekara. Wannan shi ne karon farko da wani kamfani ya sayi damar sanya sunansa a jikin rigar furatis na kwallon kafa a Ingila.

3. Man U na samun abinda bai kasa dala miliyan 39 ba kowace shekara daga kamfanin NIKE wanda ke sayar da riguna da huluna da sauran abubuwan dake dauke da suna da tambarin Manchester United.

XS
SM
MD
LG