Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Ci Gaba Da Zama a Saman Teburin Premier Bayan Yin Canjaras Da Liverpool


Kocin Manchester United Ole Gunner Solskjaer

Manchester United ta ci gaba da mallake saman teburin gasar Premier League bayan da ta tashi canjaras da tsohuwar abokiyar hamayyarta Liverpool a filin wasa na Anfield.

Sai dai a wasan, wanda bangarorin suka yi ta kai wa juna hare-hare, United ta so ta shammaci Liverpool amma mai tsaron ragar Liverpool Alisson ya hana.

Hakan na nufin kwallayen Bruno Fernandes da na Paul Pogba da Alisson ya doke, sun sa Liverpool ta ci gaba da rike tarihinta na rashin shan kaye a gida.

Yanzu kungiyoyin sun samu maki daya-daya. Ita dai Liverpool, ita ke rike da kofin gasar.

Yanzu United na da maki 37 yayin da Liverpool take da maki 34, wato suna da tazarar maki 3 kenan a tsakaninsu.

Sauran wasannin da aka buga a karshen makon da ya gabata, Wolverhampton Wanderers ta sha kaye a hanun West bromwich Albion da ci 3-2.

Chelsea ta doke Fulham da ci daya mai ban haushi yayin da ita kuma Westham United ta doke Burnley da ci daya da banza.

Tottenham ita ma ta lallasa Shieffield United da ci 3-1. Manchester City kuma ta lallasa Crystal Palace da ci 3-0.

Diego Maradona 1960-2020
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00
Karin bayani akan Diego Maradona
XS
SM
MD
LG