Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maniyatta da Dama Sun Rasa Rayukansu Sanadiyar Tattake Juna


Gawarwakin maniyatta da wadanda suka jikata a tattake juna da ya auku a Minna

Tattake juna da ya auku shi ne hadari na biyu a wannan aikin hajjin bana. Can baya naurar gini da ta fado ta hallaka maniyatta fiye da dari cikinsu har da 'yan Najeriya shida.

Bayan kammala jifan shaidan sai labari ya kai inda wasu maniyatta ke zaune cewa wasunsu sun rasa rayukansu sanadiyar tattake juna.

Lamarin bai rasa nasaba da cikowa da aka samu kan hanyar shiga gadoji kusan hudu na zuwa wurin jifar shaidan da ake farawa bayan hawan arafa.

Kawo yanzu dai ba'a samu cikakken labari dangane da alhazan da suka mutu da kuma kasashen da suka fito ba domin hanyoyin doshe zuwa gadar kan hada kowa da kowa.

Wannan hadarin ya auku ne a wasu hanyoyi kusa da tantunan masu hannu da shuni inda akan tare hanya da wasu alhazan kan yi kokarin samun mafita ko mashiga mai sauki.

Bana hukumar alhazan Najeriya bata zaunar da alhazanta a tantuna masu tsadar gaske ba. Usman Shamaki na hukumar alhazan na ganin hakan yayi daidai.

Yace shekaru goma ko fi da suka wuce ba'a taba raba ma'aikatan hukumar alhazai da alhazan ba. Ana zama tare dasu domin a fahimci abubuwan da suke ciki. Saboda haka dawo da jami'an hukumar cikin alhazai ya yi daidai.

Tun farko kafin aukuwar hadarin likitan alhazan Najeriya Dr Ibrahim Kana ya bayyana lafiyar alhazan gabanin hawan arafa. Alhazan suna cikin koshin lafiya ban da mutane 22 da suka rasu saboda rashin lafiya.

Mutuwar mutane sanadiyar tattake juna ya sa wasu alhazan suna waya gida saboda sanarda 'yanuwa halin da suke ciki.

Wani Aliyu Muhammad da ya tsira daga tattake junan ya kara haske akan abun da ya faru. Yace tare suka fadi da wasu da suka rasu.Ya ga mutane hudu dake gabansa da suka mutu.

Hukumar alhazan Najeriya tana taro saboda kidigdige yawan 'yan Najeriya da hadarin ya rutsa dasu. Bayanai na nuna cewa mutanen da suka rasu suna da dama cikinsu har da fitattun mutane. Daidai tantunan 'yan gata ne lamarin ya auku.

Wani bidiyo da jami'an kiwon lafiyar Saudiya suka fitar ya nuna gawarwaki a kwance kimanin tsawon kilomita daya da adaddin mutuwar da aka yi ta kai mutum dubu daya. Ana fargaban wani farfasa da wata shahararriyar 'yar jarida na cikin wadanda suka mutu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:04 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG