Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Hafsoshin mayakan Najeriya Sun Isa Birnin Maiduguri.


Rundunar Sojojin Najeriya
Rundunar Sojojin Najeriya

Manyan hafohin mayakan Najeriya sun isa birnin Maiduguri a jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria biyo bayan umarnin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo cewar manyan sojojin su koma yankin da ya sha fama da hare haren yan ta’addan Boko Haram tare da yin garkuwa da mutanen yankin.

Mukaddashin shugaban kasar ya bada wannan umarni ne domin tabbatar da ganin an maido da zaman lafiya a wannan yanki. Manyan sojojin sun gudanar da wata tattaunawar sirri tsakaninsu na ganin yadda za a kamo bakin zaren da kuma kawo karshen irin wannan matsala na ta’addanci baki daya.

Bayan kwashe tsawon awa hudu ana tattaunawa tsakanin manyan hafsoshin sojan kasar karkashin jagorancin hafsin hafsoshin sojojin Najeriya Janar Ilorin Shekin, sai mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Manjo Janar John Anache ya yiwa manema labarai bayani game da ziyararsu da kuma abin da suka sa a gaba.

Darektan hulda da jama’a na rundunar sojan kasar Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, yace har yanzu rundunar sojojin Najeriya tana kan bakanta bisa wannan aiki kuma suna neman hadin kai da goyon bayan jama’a musamman wurin basu bayanai da zau taimaka, kamar yadda suke zaton akwai Boko Haram na zaune tare jama’a, don haka kowa ya sa ido kuma ya kai labari ga jami’an tsaro idan ya gano irin wadannan mutane.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG