Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jami’an Ma’aikatar Tsaron Amurka Sun Bayyana Damuwa Akan Amfanin Da Soji Domin Siyasa


Manyan jami’an ma’aikatar tsaron Amurka na da da na yanzu sun bayyana damuwa akan amfanin da sojoji saboda dalilai na siyasa, a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanr da zanga-zanga a kasar a kan zaluncin da ‘yan sanda suke yi, yayin da suke jaddada bukatar yin adalci ga ko wane ba’amurke da kuma kiyaye rantsuwar kare ‘yancin fadar albarkacin baki da taruwar jama’a kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba da dama.

“Idan har zamu cika hakkokin da suka wajaba a kan mu a matsayinmu na masu yiwa kasa aiki, a matsayin mu na Amurkawa da mutane na gari, to dole ne mu dauki rantsuwar da muka yi da muhimmancin gaske,” shugaban Dogawaran tsaron kasar Joseph Lengyel ya fada. “Ba za mu yarda da wariyar launin fata ba da nuna bambanci ko tashin hanakali.

An tura dakarun tsaron kasa a jihohi 31 don taimakawa jami’an tsaron yankin a kan zanga-zangar da ta fara a makon daya da ya gabata sakamakon mutuwar ba’amurke bakar fatar George Floyd a hannun ‘yan sanda.

Shugaba Donald Trump ya bukaci gwamnonin kasar da su turo dogarawan tsaron kasa zuwa Washington DC, kana Sakataran Tsaron Amurka, Mark Esper ya baiwa dakaru dubu 1,300 da suke aiki umarnin su koma sansanonin wajan babban birnin Amurka inda aka saka a zaman jiran ko ta kwana idan ana bukatar su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG