Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Raguwar Mutuwa Ta Dalilin Kanjamau


Survivors say a suicide bomber disguised in a school uniform detonated explosives at a high school assembly, Potiskum, Nigeria, Nov. 10, 2014.

Wani sabon ruhoto mai suna ‘kusa da ziro da cibiyar yaki da cutar kanjamau na majalisar Dinkin Duniya ya rubuta ya nuna cewa an sami raguwar mutuwar masu fama da cutar kanjamau sun ragu domin karin amfani da maganin rage karfin cutar a sashin duka.

Wani sabon ruhoto mai suna ‘kusa da ziro da cibiyar yaki da cutar kanjamau na majalisar Dinkin Duniya ya rubuta ya nuna cewa an sami raguwar mutuwar masu fama da cutar kanjamau sun ragu domin Karin amfani da maganin rage karfin cutar a sashin duka.

Ruhoton ya bayyana cewa Karin kashi-goma na maganin rage karfin cutar ya taimaka wajen raguwar mutuwar masu fama da cutar kanjamau da kuma kara tsawon rai ga wadanda ke dauke da cutar. Ruhotun kuma ya kara bayyanawa cewa kasashe da yawa da suka hada da Botswana, Ethiopia, Kenya, Namibia, Rwanda, Zambia da Zimbabwe sun sami raguwar mutuwar masu fama da cutar da kimanin kashi 50% tun 2005. Hakanan an sami raguwar mutuwa ta tarin fuka da kashi 30% daga adadin wadanda suka mutu a tsakiyar shekaru ta 2000.

Yawan kamuwa da kwayar cutar HIV tsakanin kananan yara ya ragu zuwa rabi daga shekara ta 2001 zuwa 2011. Wannan raguwar ta samu ne ta wurin kara kula da kiyayew yada cutar tsakanin uwa-da-danta na HIV a kudanci da gabashin Africa. Irin wadannan ayyukan sun karu zuwa kashi 72% a shekara 2011 wanda yasa kusan mata masu ciki 700 000 suke rayuwa da cutar HIV amma sun sami maganin kiyaye jariran su daga HIV.

Bisa ga wannan ruhoton, an sami raguwar mutuwar masu fama da cutar kanjamau ne ta dalilin kara amfani da maganin rage karfin cutar ta kanjamau. Yawan mutane dake rayuwa da cutar dake amfani da maganin rage karfin cutar ya karu daga 625 000 a shekara ta 2005 zuwa miliyan 6.3 a 2012 da kuma yawanci a manyan wurare na kasashe hadi da Botswana, Namibia, Rwanda, Swaziland da Zambia.

Ruhoton ya kuma bayyana cewa, sababbin kamuwa tsakanin manya ya ragu daga miliyan 1.7 a shekara ta 2001 zuwa miliyan 1.2 a shekarar 2011 –– da kuma kimanin raguwar kamuwa fiye da kashi 50% a kasashe bakwai –– Botswana, Ethiopia, Malawi, Namibia, Rwanda, Zambia da Zimbabwe.

Duk da raguwar yawan HIV tsakanin mata da maza (shekaru 15–24), sabbin kamuwa cikin matasa yana nan a matsayinsa na 450 000 kamar yadda aka bada ruhoto a shekara ta 2011. Wannan ruhoton kuma ya nuna cewa abin yafi shafar matasan mata (tsakanin shekaru 15–24) a kudanci da gabacin sashin Africa. An yi kiyasin cewa yawan matasa maa dake kamuwa da kwayar cutar HIV ya kai kashi 4.5% a shekara ta 2011 wanda yafi kashi biyu na matasan maza.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG