Accessibility links

Manyan Malaman Islama Na Najeriya Sun Bayyana Goyon Baya Ga Yaki Da Polio


Ma'aikatan lafiya su na shirin digawa yara a Kano maganin rigakafin kamuwa da cutar shan inna, Polio

A bayan da suka halarci taron duniya kan yaki da cutar Polio a daular Abu Dhabi, malaman na Musulunci sun yi bitar mako guda ma 'yan'uwansu malamai a Abuja

Manyan malaman addinin Musulunci na Najeriya da suka halarci taron yaki da cutar Polio na duniya da aka yi a daular Abu Dhabi, sun gudanar da wata bitar mako guda a Abuja, babban birnin Najeriya, domin su fadakar da sauran 'yan'uwansu malamai irin muhimmancin dake tattare da tinkarar wannan cuta.

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Hafizan al-Qur'ani ta Najeriya, Sheikh Musa Hassan, yana daya daga cikin wadanda a can baya suka yi adawa suka ki yarda da wannan allurar rigakafin, amma a yanzu yace ya gamsu dari bisa dari da wannan magani, kuma ya amince da cewa tilas ne a kawar da wannan cuta daga duniya baki daya, ba ma Najeriya kawai ba.

Shugabar Kungiyar Musulmi Mata ta Najeriya, maryam Idris Othman, ta ce yana da muhimmanci a wayar da kan mata domin shawo kan maza masu kin jinin wannan allurar rigakafin.

Ga cikakken rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko daga Abuja kan wannan taron bita da irin bayanan da shaihunan malaman suka yi.

XS
SM
MD
LG