Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jami’an Najeriya Sun Marabci Kubutattun 'Yan Matan Dapchi


Janar Rogers dauke da daya daga cikin daliban

Kubutattun 'yan matan Dapchi da iyayensu da 'yan'uwa da abokan arziki da jami'an gwamnati da sauran masu fada a ji na cike da farin cikin sakin akasarin 'yan matan Dapchi da kungiyar Boko Haram ta yi. To amma kuma wasu 'iyayen na bakin cikin mutuwar 'ya'yansu.

Bayan sake akasarin dalibai mata na garin Dapchi da ‘yan Boko Haram su ka yi, manyan jami’an gwamnatin Najeriya, karkashin jagorancin Ministan Labaran Najeriya Lai Mohammed, su ka tashi daga Abuja zuwa Maiduguri, hedikwatar jahar Borno daga nan kuma su ka tafi da su zuwa babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja.

Daya daga cikin daliban da su ka yi sa’ar sake komawa ga iyayensu ta ce ‘yan Boko Haram sun maida su ne da misalign karfe 8 na safe su ka kawo sub akin tasha su ka aje su. Ta ce sun gaya masu cewa sun maida su ne saboda su Musulmai ne. Ta ce sun ba su abinci yadda ya kamata kuma ba su kuntata masu ba kodayake sun yi ta jele da su daga nan zuwa nan. Sauran matan ma sun tabbatar da wannan bayanin.

To saidai wani abin takaici kuma shi ne biyar daga cikin ‘yan matan sun mutu tun a ranar da aka sace su saboda dalilan da su ka hada da galabaita da dimuwa da dai sauransu. Alhaji Inuwa Garba Bayamari na daya daga cikin iyayen da su ka rasa ‘ya’yan nasu. Ya ce kodayake diyarsa na daya daga cikin dalibai biyar da su ka mutu, alhamdulillahi tun da akasari sun dawo.

Ga dai Haruna Dauda da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG