Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Gidauniya Complete Care Zata Tallafawa Marayu Da Mata Da Suka Rasa Mazansu


Gidauniyar Complete Care ta tallafawa mata dubu daya a jaha r Barno.

Giduaniyar zata kashe akalla milyan 200 domin tallafawa akalla mutane dubu 10

Shugabannin gidauniyar da ake kira "Complete Care" da turanci ta ce burinta ne ta taimakawa mata da marayu wadanda rikicin Boko Haram ya jefa su cikin mawuyacin hali. Akalla mutane dubu 10 ne zasu amfana karkashin shirin.

Shugabannin kungiyar suka ce zasu kuma tallafawa akalla makarantu dubu biyar.

Da suke magana da wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda, shugabannin suka ce zasu sa ido kan yara wadanda suke fama da 'yunwa da karancin abinci mai gina jiki.

Shirin zai kuma taimaka wajen gudanar da shirin musayar dalibai daga sassan kasar daban daban.

Daga karshe kungiyar Complete Care ta yi kira ga sauran kungiyoyi da su shigo su taimakawa gwanati a yunkurin da take yi na sake farfado da wannan yanki.

Ga rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG