Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martanin 'Yan Jihar Legas A Kan Jadawalin Zaben Shekarar 2019


Shugaba Muhammadu Buhari yana taya shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Mahmoud Yakubu jim kadan bayan rantsar da shi a Abuja, 9 Nuwamba 2015.

Jadawalin zaben shekarar 2019 da za'a gudanar a Najeriya ya sa wasu a Lagos na ganin tamkar hurawa 'yan siyasa usur ne da yanzu zai sa su karkata hankalinsui kan zaben ne maimakon su ci gaba da yiwa kasa aiki

Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta fitar da jadawalin zabukan shekarar 2019.

Jadawalin ya nuna za'a fara da zaben fidda 'yan takara na jam'iyyu daga ranakun 18 ga watan Agusta zuwa ga bakwai ga watan Oktoba na wannan shekarar.

Za'a gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisu da gwamnoni a ranar 16 ga watan Fabrairun badi, wato shekarar 2019 da biyu ga watan Maris na shekarar.

Tuni 'yan Najeriya suka fara mayar da martani akan jadawalin. Wasu na cewa har yanzu akwai 'yan siyasa da basu cika alkawuran da suka yi ba saboda haka zasu hadu dasu a mazaba.

Wani Useni ya ce gaskiya wasu da suka zaba lokaci ya kure masu basu tabuka komi ba, kuma yanzu hankulansu zai koma ne kan zabukan dake tafe domin neman cin zabe. Useni ya kara da cewa can baya sun yi jam'iyya sak amma yanzu zasu diba su ga wanene ya cancanta saboda suna gudun su zabi wani har lokacinsa ya kure bai yi komi ba..

Dangane da shugaban kasa a cewar Useni ya yi kokari akan Boko Haram amma sauran abubuwan kuma watakila nan gaba zai yisu.

Shi kuwa Malam Muhammad Nasir ya ce kalubalen 'yan siyasa ne musamman ma gwamnatin kasar. Alkawuran da gwamnatin ta dauka can baya, wai bata yi komi ba. Amma yanzu tunanen yadda zasu ci zaben gaba ke ransu. Harkar Boko Haram kadai gwamnati ta taka rawar gani amma a tattalin arziki, da hawa hawar farashi da kuncin rayuwa sai dai a duba don Allah, inji Nasir.

Sai dai wasu 'yan Najeriya basu amince da jadawalin ba. Alhaji Ado Dansudu wani shugaban kungiyar 'yan arewa mazauna kudu maso yammacin Najeriya yana ganin an yi saurin fitar da jadawalin.Kamata ya yi a jinkirta zuwa tsakiya ko karshen shekarar. A ganinsa an kada gangar zabe ne yanzu.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG