Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Marwana Yace Shi Ya Bada Umurnin Kai Hari Na Kano


Mutane su na kallo a inda aka kai harin bam a Unguwar Sabon Gari dake Kano
Mutane su na kallo a inda aka kai harin bam a Unguwar Sabon Gari dake Kano

Muhammadu Marwana yayi ikirarin cewa an kai harin ne don nunawa masu shakkar sahihancinsa cewa zasu iya, koda yake babu hanyar tabbatar da gaskiyar kalamunsa

Mutumin dake ikirarin cewa a yanzu shi ne shugaban rikon kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram, Muhammadu Marwana, yayi ikirarin cewa shi ne ya bayar da umurnin kai harin makon da ya shige a unguwar Sabon Gari dake Kano, cibiyar kasuwanci ta arewacin najeriya.

A lokacin da yake hira ta wayar tarho da VOA Hausa, mutumin mai kiran kansa Marwana, yace akwai wadanda suka bayyana shakkar sahihancinsa, kuma tun kafin a kai wannan harin, sai da ya sanar da wadanda ke shakkar maganarsa cewa za a kai shi. Yace dalili shi ne ana samun kwan-gaba kwan-baya a kan maganganun da suke yi, shi ya sa suka dauki wannan matakin.

Sai dai yayi gargadin cewa ba su kadai ne 'ya'yan kungiyarsu suke kai irin wadannan hare-haren ba, domin akwai masu fakewa da shi domin tabbatar da cewa ba a toshe musu hanyoyin samu ba.

A kan ko wannan batu na harin Sabon Gari koma-baya ne tunda shi da bakinsa yayi alkwarin cewa ba za a sake samun hakan ba, sai mutumin yace ba koma-baya ba ce domin kashedi ne.

Babu wata hanya ta dabam, ko wata kafa mai zaman kanta, ko ta tsaro, da ta gaskata kalamu da kuma ikirarin da shi wannan mutumi yake yi.

Marwana Yace Shi Ya Bada Umurnin Kai Hari Na Kano - 1:53
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:53 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG