Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana A Nijar Sun Bayyana Ra’ayoyinsu Akan Harin Ta’addanci


Motocin Yakin Faransa akan hanyarsu ta zuwa bakin iyakar Nijar kusa da garin Gao, a Mali. Fabrairu. 6, 2013
Motocin Yakin Faransa akan hanyarsu ta zuwa bakin iyakar Nijar kusa da garin Gao, a Mali. Fabrairu. 6, 2013

Ran Alhamis dinnan ne aka kai tagwayen hare-haren kunar bakin wake a garuruwan Agadas da Arlit, garuruwan da ke da cikakken matakun tsaro.

Farfesa Ado Muhamman, Malami a Jami’ar Birnin Yamai yace wannan hari da ‘yan ta’adda suka kai, suna da wata manufa.

“Suna so sub a kasashe tsoro, su razana kasashe sosai, domin su ci karensu babu babbaka. Shi fada, da yaki dan yaudara ne, in ka bari, sai a yaudare ka, a yi maka zamba.” A cewar Farfesa Ado Muhamman.

Ra’ayoyin sun bam-bamta. Malam Muhammadu Juri na wata kungiyar fararen hula yace dole sai an sauya salon siyasa a Nijar sannan za’a iya kiyaye irin wadannan hare-hare.

A jiya Alhamis ne wasu motoci dankare da bama-bamai sun tarwatse a mashigar barikin sojan garin Agadez da garin Arli, inda mutane kimanin 20 su ka riga mu gidan gaskiya, baya ga da dama da su ka sami raunuka.

Kungiya mai tsatsaurar ra'ayin Islama, MUJAO a takaice, ita ce ta dauki alhakin wannan hari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG