Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Na Ci Gaba Da Yin Tsokaci Kan Batun Tsaro a Najeriya


'Yan bindiga
'Yan bindiga

A Najeriya, karuwar hare haren da ‘yan fashin daji ke yi a jihohi irinsu Kaduna, Neja, Kogi, har ma da Abuja babban birnin tarayyar kasar sun janyo fargaba da damuwa musamman ganin yadda ‘yan bindiga dauke da manyan makamai ke tafiya daga wani bangaren zuwa wani.

Abuja, Najeriya - Yanayin tabarbarewar tsaro da yankin arewancin Najeriya ke fuskanta na neman kai wankin hula dare, la’akari da yadda hare haren ‘yan bindiga da masu satar mutane domin karbar kudin fansa ke kara muni.

Kwanaki kadan bayan wani mummunan hari da aka kai kan wani jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, an ga wani gungun ‘yan bindiga suna wucewa kan babban titin da ya hada jihohin biyu, duk kuwa da jibge jami’an tsaro da gwamanti ta yi tun bayan faruwar lamarin.

Masanin lamuran tsaro Manjo Yahya Shinku Mai ritaya, ya ce lamarin tsaro na neman ya kwace musamman a yankin jihar Kaduna zuwa Abuja, don haka ya kamata gwamnati ta fuskanci matsalar sosai ta hanyar kara yawan sojoji a yankin, bayan haka duk aikin da za a yi a yi shi bai daya.

Rahotanni sun yi nuni da cewa an yi arangama tsakanin wasu ‘yan bindiga da sojoji a kusa da garin Suleja inda suka kashe sama da soji 9 tare da raunata wasu, lamarin ya bayyana ne cikin wani bidiyo da aka yi ta yadawa ta shafukan sada zumunta da ma wadanda suka gani da idonsu. Ko da yake rundunar sojin kasar ba ta tabbatar da hakan ba ko ta musanta.

Tsohon dan majalisar dokoki daga jihar Kaduna ta tsakiyar, Shehu Sani, ya bayyana cewa wannan matsala zata iya lakume kowa da kowa idan har ba a gaggauta daukar mataki ba. An kashe fiye da naira Tiriliyan hudu cikin shekara 7 don magance matsalar tsaro da kare rayukan jama’a amma har yanzu ana ci gaba da zubar da jini, a cewarsa.

Shi ko Dakta Yahuza Ahamed Getso, kwararre kan sha’anin tsaro a Najeriya, cewa ya yi akwai sakaci da yashe kafa a lamarin tsaron Najeriya, don akwai tabbacin cewa akwai masu yin bita da kulli a cikin gwamnatin kasar.

Sanata Ali Ndume, da ke zama shugaban kwamitin soji a majalisar dokokin tarayya, ya yi kari da cewa kowa na da rawar da zai taka wajen magance matsalar tsaro, saboda duk da kokarin da jami’an tsaro ke yi akwai bukatar a taimaka musu da bayanai.

A halin da ake ciki, lamarin matsalar rashin tsaro da ke dada tabarbarewa ya haifar da fargaba ga matafiya musamman wadanda ke bin hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

XS
SM
MD
LG