Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Shari'a Na Ganin Madogarar Saraki kan IPOB Ba Ta da Karfi


Dr. Bukola Saraki, shugaban Majalisar Dattawan Najeriya
Dr. Bukola Saraki, shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Bayan da sojojin Najeriya suka ayyana kungiyar IPOB, mai fafutikar kafa kasar Biafra daga Najeriya, a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr. Bukola Saraki ya fito karara ya ce matakin da sojojin suka dauka ya sabawa dokar kasa.

Masana dokokin kasar Najeriya na cigaba da yin tsokaci kan kalamun Dr. Bukola Saraki shugaban Majalisar Dattawan Najeriya dangane da ayana kungiyar IPOB mai fafutikan kafa kasar Biafra a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Makon jiya ne rundunar sojojin Najeriya ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda. Haka ma gwamnonin jihohin kabilar Igbo su ma suka ayyana kungiyar cewa ta ta'addanci ce suka kuma haramtata saboda yadda take yiwa sha'anin tsaron kasar barazana.

Amma kwatsam sai shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr. Bukola Saraki ya fito fili baro-baro ya ce ayyana IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda ya sabawa kundun tsarin mulkin Najeriya.

Wani masanin kundun tsarin mulkin Najeriya Barrister Danlami Wushishi na ma'aikatar kiwon lafiyar jihar Neja ya ce shugaban Majalisar yana da 'yar madogara amma ba mai karfi ba ce. Yana mai cewa akwai dokar majalisar tarayya da ta ce kafin a ayyana wata kungiya a matsayin ta ta'addanci sai an je kotu, kotun kuma ta amince.

Sai dai a cewarsa idan an jira a shigar da takardu kotu za'a bata lokaci. Amma tun da sojoji ne suka ayyana haka kana gwamnonin jihohin kabilar Igbon suka sake jaddada cewa kungiyar ta ta'addanci ce bisa yin la'akaci da tashin tashinar da take harzukawa, matsayin shugaban majalisar na da rauni. Yace gwamnonin sun fi kowa sanin yadda 'yan kungiyar IPOB din suke, sun sansu, sun san muggayen ayyukan da suke yi.

A halin yanzu gwamnatin jihar Neja ta dauki matakan wayar da kawunan jama'a dangane da mahimmancin zaman lafiya tare da juna. Yakamata a yi hakuri da juna saboda jihar tana da 'yan kabilar Igbo da yawa masu harkokin kasuwanci.

Jibril Baba Ndati kakakin gwamnan jihar Neja yana mai cewa gwamnan jihar ya gargadesu kada su bi wadanda suka kauce hanya suka maida martani a kudu maso gabashin kasar. A jihar kada a taba kabilar Igbo dake zaune lafiya da kowa. Haka ma Joshua dan kabilar Igbo ya shawarci matasan kabilarsa dake can jihohin Igbo din su bar kowa ya zauna lafiya a kasar Najeriya. Kungiyoyi ma da shugabannin jama'a a jihar Neja na cigaba da jaddada mahimmancin zaman lafiya da hadin kan kasar.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG