Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Ce Kasashen Afirka Za Su Yi Matukar Juyayin Mutuwar Sarauniyar Ingila


Sarauniyar Ingila Elizabeth II
Sarauniyar Ingila Elizabeth II

Masanin kimiyyar siyasar duniya na jami’ar Bayero ta Kano Dr. Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce kasashen Afurka da dama za su yi juyayin mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu don rawar da ta taka wajen karbar ‘yancin su.

ABUJA, NIGERIA - Dr. Dukawa ya kara da cewa yawancin mutane sun tashi da jin sunan sarauniyar wacce ta zo da kan ta ziyarar aiki kasashen kuma ta kulla hulda mai karfi da manyan jagororin kasashen wadanda akasarin su, sun dade da barin duniya “duk mai shekara 40 zuwa 50 har 70 ya tashi ya na jin sunan sarauniya Elizabeth, don haka yau an wayi gari mai irin wannan matsayi ta kau daga duniya”.

Dukawa na ganin samun cike gurbin da marigayiyar ta bari na da wuya don yanda ta dade da samun gogewa a tsawon shekaru sai dai a na fata sabon sarki, magajinta Charles ya samu gogewa ko tarbiyantuwa daga mahaifiyar ta sa.

Sabon Sarkin Ingila Charles
Sabon Sarkin Ingila Charles

Marigayiya Elizabeth ta yi mu’amalar kirki da iyayen Najeriya irin marigayi Firai Minista Abubakar Tafawa Balewa da Firimiya Ahmadu Bello Sardauna har da ba su lambar girmamawa ta masarautar Ingila da aka ambatawa ko rubutawa gabanin sunan su wato SA ko kuma SIR a turance.

Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Masana Sun Ce Kasashen Afirka Da Dama Za Su Yi Matukar Juyayin Mutuwar Sarauniyar Ingila.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

XS
SM
MD
LG