Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Taurari Sun Gano Wani Babban Kogi A Duniyar Taurari


Hoton nan na tauraruwar Titan dake Duniyar Saturn da kumbon Cassini na Turai ya dauka.
Kumbon kasa da kasa da ake kira Cassini da yake gewaya duniyar Saturn da taurarinta tun 2004, ya aiko da bayanai dalla-dalla masu muhimmanci na wani kogi shigen kogin Nilu a kan wata tauraruwar da take kan duniyar ta Saturn. Kogin yana da tsawon kilomita dari hudu daga inda ya samo asali, kuma ya kare cikin wani teku.

Hukumar binciken sararin samanaiya ta turai tace wannan ne karo na farko da masana taurari suka ga siffar kogi mai girma haka a wani wuri ba a doron kasa ba.

Masana kimiyya suka ce kogin yana cike da wani sindari mi shigen ruwa kamar yadda ya fito cikin wata na’ura mai karfi na hangen nesa da alamar baki baki a duk tsawon kogin, da ya nuna samansa yana nan sumul.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG