Accessibility links

Masana Sun Gargadi Mata Kan Kayyade Haihuwa


Wasu mata masu ciki suna jiran ganin likita

Masana sun bayyana cewa daya daga cikin hatsarorin da mata suke fuskanta da ya hafi rayuwarsu shine yawan haihuwa.

Masana sun bayyana cewa daya daga cikin hatsarorin da mata suke fuskanta da ya hafi rayuwarsu shine yawan haihuwa. Bisa ga cewar masana, mata sukan fara shiga cikin hatsari idan suka haihuw fiye da sau shida. Daga wannan lokacin haihuwa tana kara zama da hasari.

Hatsarin haihuwa yafi yawa tsakanin matan da suke haihuwa kafin shekarunsu ya kai na haihuwa watau matan da ake yiwa aure da wuri tun kafin jikinsu ya yi karfi na daukar ciki da haihuwa, da kuma matan da suka tsufa karfin jikinsu ya ragu.

Wannan na nufin cewa, fiye da rabin yaran da aka Haifa suna da hatsarin mutuwa kamin suyi shekaru biyar nasu na farko. Abinda zai taimaka wajen ceton irin wadannan jariran shine, kayyade iyali da kuma bata rata tsakanin haihuwa da haihuwa.

Masanan sun bayyana cewa, daukar matakin ceton rayukan mata da kananan yara ta wajen kayyade iyali yana da amfani na ga rayuwar matan kadai ba, amma har da al’umma da kuma kasa da duniya baki daya, domin zai rage mutuwa ta cututtuka. Zai kuma taimaka wajen inganta tattalin arzikin kasa.

An kiyasta cewa, ya zuwa 2015, adadin al’ummar Nigeriya da ba’a Haifa ba tukuna zai kai miliyan 94 da kuma adadin wadanda ke a kauyuka zai kai kimanin miliyan 82.
XS
SM
MD
LG