Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Yi Na'am Da Shirin Rage Cunkoso A Gidajen Kason Najeriya


Abubakar Malami ministan shari'a na Najeriya kuma antoni janar

A ziyarar aiki da ta kai shi Kano, Ministan Shari'ar Najeriya, Abubakar Malami, ya amince da sakin wasu furusinoni kusan dari hudu dake gidan kaso a Kano abun da masana harkokin shari'a suka yi na'am da shi amma suka ce hakan ba zai yi wani tasiri ba idan ba'a dauki wasu matakai ba.

Gwamnatin Najeriya tayi afuwa ga wasu daurarru guda 368 dake tsare a gidan yari na Kurmawa dake Kano, a wani mataki na rage cunkoso a gidajen yarin kasar.

Sai dai masana dokoki da shari’a sun ce akwai bukatar gwamnati ta dauki wasu karin matakai domin magance matsalar cunkoso a gidajen kurkuku na Najeriya da kuma kiyaye aikata laifuffuka a cikin al’umma.

A yayin ziyarar aiki a Kano, babban atoni janar kuma ministan shari’a na tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, bisa rakiyar shugaba da wakilan kwamitin gwamnatin tarayya kan rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya, ya sanar da matakin yin afuwar ga daurarrun su kimanin 400.

Wannan dai shine karo na biyu da gwamnatin tarayyar ke yin afuwa ga daurarru a Kano cikin kasa da watanni biyu da suka shude.

Kodayake masana harkokin shari’a sunyi na’am da wannan yunkuri, amma sun ce ba zai yi tasirin da ake muradi ba na rage cunkoso a gidajen yari a Najeriya, kamar yadda tsohon magatakardan babbar kotun Kano, Barrister Abdullahi Sufi, ke fadi. Yana cewa akwai abubuwan da ya kamata a duba domin a rage cunkoso a gidajen kaso. Wadandan ko su ne harkokin alkalai, 'yan sanda, ma'aikatan shari'a da mutanen gari. Akwai bukatar a gina wasu gidajen kaso.

'Yan sanda na juya maganar da aka kai musu domin su tsare mutum gidan kaso. Alkalai ma na da tasu rawar da suke takawa. Inji Barrister Sufi bincike bai kamata ya dauki wani tsawon lokaci mai yawa ba. A ma'aikatar shari'a sai a yi shekara shida zuwa bakwai ba'a samu amsar da ake bukata ba domin shari'a ta ci gaba

Shi kuwa lauyan gwagwarmayar kare hakkin bil’adama a Kano Barrister Audu Bulama Bukarti cewa yayi matakin ya yi dai-dai da tanadin dokokin kasa, amma akwai bubuwan dubawa dangane da mutanen da za'a sako. Ya ce ana iya a samu matsala idan mutaen gari sun ki karbarasu. Su kansu mutanen idan sun saba da gidan kaso inda suke samun abinci da wurin kwana ba sai sun biya ba zama cikin jama'a inda sai sun nemi nasu ka iya zama wahala.

A watan disamban da ya shude ne dai shugaba Buhari da kansa ya yi afuwa ga wasu daurarru lokacin daya kawo ziyarar aiki Kano.

Haka shi gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi afuwa ga daurarru 500 a lokacin bukukuwan sallah babba da aka yi a watannin baya.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG